Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Ta Ce Sojojin Najeriya Sun San Za A Kai Hari A Chibok, Amma Ba Su Yi Komai Ba - 9/5/2014


Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce shaidar da ta tattara ta nuna cewar dakarun tsaron Najeriya sun kasa daukar matakin yin rigakafi, duk da gargadin da suka samu cewa ga ‘yan Boko Haram sun doshi Chibok a daren 14 ga watan Afrilu.

Darektan bincike game da Afirka na kungiyar, Netsanet Belay, yace ganin cewa sojoji sun san cewa za a kai wannan harin amma ba su dauki matakan hanawa ba, yin watsi da nauyin dake wuyarsu na kare fararen hula ne, wadanda ke fuskantar irin wadannna hare-hare. Yace tilas shugabannin Najeriya suyi amfani da dukkan halaltattun hanyoyi na tabbatar da cewa irin wannan bai sake faruwa ba.

Kungiyar Amnesty ta ce ta tabbatar ta hanyoyi da dama cewa tun karfe 7 na maraicen 14 Afrilu, hedkwatar sojoji dake Maiduguri, da kuma rundnar sojan dake garin Damboa, kilomita 37 daga Chibok, sun samu labari daga majiyoyi da yawa cewa ga 'yan bindiga sun doshi garin Chibok. Wasu manyan hafsoshin sojan Najeriya biyu sun gaskata wannan labarin in ji Amnesty.

Amma sai aka bar sojoji kwaya 17 dake Chibok kawai da 'yan sandan garin suka yi fada da wadannan 'yan bindiga ba a kai musu dauki ba. Su kuma da aka fi karfinsu, suka ja da baya.
XS
SM
MD
LG