Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Hudu Suka Yi Alkawarin Taimakawa Najeriya Ya Zuwa Yanzu Kan Boko Haram - 8/5/2014


Michelle Obama tana nuna goyon bayanta ga kwato dalibai mata na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace
Michelle Obama tana nuna goyon bayanta ga kwato dalibai mata na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace
Kasashe su akalla hudu ne, cikinsu har da Amurka, suka yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen nemo dalibai mata su 276 wadanda 'yan Boko Haram suka sace.

A lokacin da yake jawabi ga taron kolin Tattalin Arzikin Duniya yau alhamis a Abuja, shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya godewa kasar China, wadda ita ce ta baya-bayan nan da ta gabatar da tayin taimakawa wajen samo wadannan dalibai mata.

Amurka, da Britaniya da kuma Faransa su ma sun bayar da tayin taimakawa.

Shugaban na Najeriya yace sace wadannan dalibai mata da 'yan Boko Haram suka yi zai zamo matakin kawo karshen ta'addanci a Najeriya.

Jiya laraba, rundunar sojan Amurka ta ce mashawartanta zasu isa Najeriya cikin 'yan kwanaki kadan domin taimakawa ta hanyar sadarwa, kayan aiki da bayanan leken asiri. Britaniya ta yi alkawarin bayarda hotunan taurarin dan Adam, yayin da Faransa ta ce zata tura jami'an tsaronta.
XS
SM
MD
LG