WASHINGTON, DC —
Cutar yoyon fitsari, na kara karuwa a jihar Kano , Najeriya, shugabar Cibiyar dake kula da mata masu yoyon fitsari, Aisha Hassan, ne ta furta haka a wata hira da Wakiliyar muryar Amurka, Baraka Bashir.
Malama Aisha Hassan, tace a cikin wata biyu a kan samun sababbin mata masu dauke da cutar yoyon fitsari, kimanin talatin, ta kuma mai cewa wadansu koda anyi masu aiki cutar baya warkewa, wanda hakan ke jawo yi masu aiki har sau biyu ko sau uku.
Daga karshe tace yawaitar masu yoyon fitsari, na ci mata tuwo a kwarya, ta kuma bukaci jama’a, da masu hannu da shuni, dasu taimaka domin kawo saukin wannanan cutar.
##caption:Mata a Cibiyar Kula da Masu Yoyon Fitsari.##