Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Plateau, ta bayyana cewa akwai dokar data tanadi biyan kudi Naira dubu dari biyar da kuma daurin shekaru biyu a gidan Yari, ga duk wanda aka kama da saye ko kwatar katin zabe daga jama’a.
Jami’in hulda da jama’a na hukamar zaben a jihar Plateau, mista Osaretin ya bayyanawa wakiliyar mu Zainab Babaji, cewar ya zuwa yanzu sun raba katuna fiye da miliyan daya da dari shida daga fiye da miliyan biyu da dari uku da suke tsammanin samu a jihar plateau. Osaretin yace guraren da suke da matsalar raba katin zabe sun hada da kananan hukumomin Kanke, Jos ta kudu, da Lantan ta arewa da Lantan ta kudu, wadanda acewarsa har ya zuwa yanzu ba’a buga katunan zaben nasu ba, yakuma bada tabbashin cewar kafin ranar takwas ga watan Maris duk jama’ar jihar zasu sami katin su.
Ata bakin jami’in hukumar zaben yace, suna da masaniyar cewa wadansu na karbar lambar kati, wadansu kuma na sayen katin zaben. Amma doka ta tanadi hukuncin biyan Naira dubu dari biyar da daurin shekaru biyu a gidan Yari, kuma babu wanda zai iya amfani da wannan katin wajen kada kuri’a, yakuma ce suna kiran masu ruwa da tsaki kan su wayar da kan jama’ar su, kar su yarda su bayar da katin su bisa ga kowanne irin dalili.