Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, yace, Obasanjo shugaba ne wanda ya shugabanci kasar a zamanin mulkin soja da kuma lokacin da aka kafa jam'iyyar PDP, ya kara da cewa kowane dan adam yana da nau'i na fushi da kuma na murna, abun da yayi ya nuna fushi ne.
Gwamna Lamido, yace gaskiya a siyasance Obasanjo uba yake garesu amma kuma akwai hakin shugabanci akansa cewa komai wuya, komai masifa komai fushi ana tsanmanin babba ya san irin fushin da zai yi. Obasanjo ubansu ne kuma ba zasu gujeshi ba, haka ma shi Jonathan da yake gareshi babu abun da zai iya yi sai dai Allah ya sawaka.
Dangane da ko zasu je su lallashi Obasanjo sai gwamna Lamido yace idan babba yayi fushi akwai ha’dari, yace yanzu mutanen kudu suna gudu daga arewa suna komawa kudu. Haka ma mutanen arewa suna gudu daga kudu suna komawa arewa, wannan lamarin yana da ban tsoro. An shiga wani yanayi yanzu sai dai manya su kara yin hakuri su kai zuciyarsu nesa, abin da za'a sa gaba yanzu shi ne yaya za'a gyara kurakuran yara da aka kawo shugabanci, domin Obasanjo shi ya kawo Jonathan, da badan haka ba bazai zama shugaban Najeriya ba.
Keta katin zama dan jam'iyyar PDP a bainar jama'a ba zai yi maganin komi ba kuma ba shi ne mafita ba. Nuna fushinsa a bainar jama'a bai kawar da gaskiyar cewa shi ne ya kawo Jonathan a siyasance ba.
Lamido, yace korar da PDP tace ta yiwa Obasanjo bayan ya fice wauta ce. Duk wadanda suke PDP yanzu 'ya'yansa ne.