Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Tace Masu Son Jigilar Alhazan Najeriya; Shari'ar Ikhwanul Muslimun A Masar; Taron kolin kasashen Larabawa - 25/3/2014


حجاج
حجاج
NAJERIYA - HAJJ -- An fara tantance kamfanonin jiragen saman da zasu yi jigilar alhazan Najeriya su dubu 74 a bana. Shugaban hukumar alhazan Najeriya, Muhammadu Musa Bello, yace akwai dalilin da yasa a bana kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka shiga cikin masu neman aikin jigilar.

NAJERIYA - AREWA -- Gwamna Murtala Nyako na Adamawa da Abdulaziz Yari na Zamfara, sun ce akwai mamaki yadda aka kasa takalar Boko Haram a Najeriya, watakila ko akwai wani abu ne da ba a sani ba.

AFIRKA - MASAR -- Shugaban kungiyar Ikhwanul Muslimun ta Masar da wasu ‘ya'yan kungiyar su kusan 700 sun gurfana gaban kotu yau talata inda aka fara musu shari’ar kisan kai da haddasa tashin hankali. Wani lauya yace a bayan ‘yan sa’o’i kadan kawai da fara shari’ar Mohammed Badie da sauran sai aka dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu lokacin da ake sa ran za a yanke hukumci. Lauyoyin dake kare mutanen sun kaurace wa zaman kotun domin nuna rashin yardarsu da hukumcin da wannan kotu ta yanke jiya litinin a birnin Minya. Kotun ta yanke humkumcin kisa a kan ‘ya’yan Ikhwanul Muslimun su 529 a bisa tuhumar kashe wani dan sanda da kai hari kan caji ofis da kuma haddasa fitina.

DUNIYA - KUWAIT -- Shirin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da ya cije da kuma yakin basasa a kasar Sham sun mamaye zauren taron koli na 25 na kungiyar kasashen larabawa da aka bude yau talata a kasar Kuwait. Wani wakilin VOA yace ana gudanar da taron kolin na yini biyu a yayin da ake kara samun sabani tsakanin ‘ya’yan kungiyar, koda yake dukkan wadanda suka yi magana, bakinsu ya zo daya wajen yin Allah wadarai da abinda suka bayyana a zaman cin zali da zarafin da Isra’ila ke ma Falasdinawa da kuma zub da jini a kasar Sham.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG