Kasar Afirka ta Kudu ta musunta cewar an shirya zata fuskanci kungiyar Super Eagles a wasan sada zumunci.
An soke wasan da aka shirya tsakanin Super Eagles da kasar Ghana, ranar 29 ga watan Maris a London, bisa dalilin sabuwar dokar da FIFA ta shimfida, cewar kasa bazatayi wasa har biyu ba cikin kwana uku a nahiya daban daban. Najeriyar dai zata kara da Bolivia a filin wasan Uyo a wannan watan, hakan yasa zasu iya wasa da kasar dake a nahiyar Afirka a cikin kwana uku bayan wasan.
Duk da haka dai manajan sadarwa na SAFA Dominic Chimhavi, ya musunta cewa akwai wata magana tsakanin kasashen biyu kan wani wasa na kawance. A lokacin dayake magana da mujallar Goal yace, “babu wani abu kamar haka da aka tsara.”
Kungiyar kwallon Afirka ta Kudu dai sunyi kunnen doki da Najeriya 2-2, a wasan su na baya da suka buga na neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka. Hakan ya sa Najeriya ta kasa samun damar kare kanta a matsayin zakaran nahiyar ta Afirka, da akayi na wannan shekarar a Equatorial Guinea.