WASHINGTON, DC —
NAJERIYA - KADUNA - Hukumomin ‘yan sanda sun nemi kakakin tsohon gwamnan Kaduna, marigayi Patrick Yakowa, Reuben Buhari, da ya bayyana musu manufarsa game da wasu hotunan kashe-kashe da ya manna a kan Facebook. ‘Yan sandan sun gayyace shi ne bisa hujjar cewa wannan abu da yayi na iya haddasa fitina.
NAJERIYA - BORNO - Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Borno, ya ziyarci inda wasu ‘yan sanda 5 suka rasa rayukansu a lokacin da suka koro wata mota dauke da ‘yan ta’adda 3 cikinta dake kokarin shiga Maiduguri. Maharan sun tayar da bam cikin motar suka kashe kawunansu da wadannan ‘yan sanda. A wani gefen, gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko na Jihar Sokoto yace mayarda sha’anin Boko Haram tamkar matsalar mutanen arewa ce kawai, ita ce ta sa aka kasa warware ta.
AFIRKA - BANGUI - Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afirka dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta ce daga yanzu zata rika daukar ‘yan bangar nan da ake kira Anti-Balaka a zaman abokan gaba. Kwamandan rundunar da ake kira MISCA, Janar Jean-Marie Michel Mokoko, shi ne ya bayyana ga wani gidan rediyon Bangui jiya talata da dare, kimanin sa'o'i 24 a bayan da ‘yan bindiga suka kashe wani sojan kiyaye zaman lafiya a Boali, mai tazarar kilomita 80 a arewa da babban birnin. Wadannan ‘yan bangar mabiya addinin Kirista sun kai hare-hare tare da kwasar ganima a unguwannin Musulmi na Bangui da wasu garuruwan kasar, inda suka tilastawa dubban musulmi guda zuwa inda zasu samu tsaro ko kuma zuwa kasashe makwabta.
AFIRKA - SOMALIYA - Sojojin gwamnatin Somaliya da na Tarayyar Afirka sun kwace garin al-Bur na tsakiyar kasar, gari na baya bayan nan da suka kwato daga hannun ‘yan tsagera na al-Shabab. Rundunar KTKA a Somaliya ta fada yau laraba cewa dakaru sun kwato wannan gari mai tazarar kilomita 350 a arewa maso gabas da Mogadishu babban birnin kasar, bayan da aka yi kwanaki uku ana gwabzawa. Rundunar ta ce dakarunta da na gwamnatin Somaliya sun ‘yanto manyan garuruwa guda 10 daga hannun al-Shabab tun lokacin da suka kaddamar da wani gagarumin farmaki kan kungiyar mai alaka da alqaida a watan da ya shige.