Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Antonio Guterre: Janye Tallafin Da Amurka Ke Yi Na Bada Taimako Abin Takaici Ne


Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya yi abin da ya kira, "matukar takaicin" janye tallafin da Amurka, ke bayarwa ga asusun majalisar dinkin duniya na taimakon bil'adama, wanda ke taimaka ma miliyoyin mata da yara a fadin duniya.

Gwamnatin Trump, ta fadi a ranar Litini cewa ba za ta cigaba da tallafa ma shirin asusun ba, saboda ta gano cewa asusun na goyon baya ko kuma taka rawa a ayyukan zubar da ciki da kuma shirin nakkasa mahaifa a China.

Mai magana da yawun Guterres, ya fadi jiya Talata cewa shugaban na majalisar dinkin duniya ya yi imanin cewa an yanke wannan shawarar ce bisa ga wata bahaguwar fahimtar da ake ma ayyukan asusun, sannan ya yi kira ga masu ba asusun gudunmowa da su ba da himma.

A shekarar 2015, asusun ya karbi gudunmowar dala miliyan 979 saboda ayyukan da ya ke yi a kasashe 150. Kasar Amurka, ta samar da kusan dala miliyan 76 ga asusun, wanda ya maida Amurka, daya daga cikin mafiya bayar da gudummwa ga asusun.

Asusun bai fito da bayanai na yadda ya kashe kudadensa jiya Talata ba, amma yana mai yin watsi da zargin na kasar Amurka, wanda ke cewa ya na goyon bayan zubar da ciki da kuma nakkasa mahaifa da ake yi a China.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG