Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba-Amurken Da Ya Kirkiro Email Ya Rasu Yana Da Shekaru 74


Ba Amurken nan Ray Tomlinson, da ya kirkiro email na zamani ya rasu yana da shekaru saba’in da hudu a duniya.

Kawo yanzu ba a bayyana masababin rasuwarshi ba.

Jagora a fannin fasaha na zahiri, Ray ne ya kawo mana email farkon kirkiro da computer” inji wani ma’aikacinshi Raytheon a wata sanarwa. Aikin shi ya canza yadda duniya ke sadarwa.”

Tomlinson ya kirkiro hanyar sadarwa kai tsaye ta na’ura a shekarar alib da dari tara da saba’in da daya, dake aiki tsakanin komputoci dabam dabam. Ya kuma zabi amfani da alamar “A” mai lauje ko kuma “at” domin hada sunan mai aika sako da adireshin da zai tura sakon, wanda yanzu ya zama alamar da ake amfani da ita a adireshin email.

Tawagar email na google, Gmail sun aika sakon twitter cewa, “Mun gode Ray Tomlinson, domin kirkiro da email da kuma sa alamar “a” mai lauje “at” a taswirar email.

XS
SM
MD
LG