Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata Samari Da 'Yan Mata Na Yi Ma Juna Kwace Ba- Inji Malama Lubabatu


Malama lubabatu Ibrahim dattijiya ce, kuma ta bada shawar wari masu ma’ana musamman ga matasa da kuma kira ga iyaye domin samun shawo kan wannan babbar matsala ta kwace saurayi daga kawav ko budurwa daga aboki wadda ta zamo tankar wutar daji.

A cewar ta, a zamanin su babu yadda budurwa zata hada ido da saurayin ta, kullum kanta a kasa yake, kawar ce za ta yi yawanci zance da saurayin nata, kuma kawar tamkar ‘yar uwa take a wurin ta.

Malamar ta kara da cewa, babu yadda za’a yi shi’awa ta shiga tsakanin saurayin kawa, domin kawa tamkar ‘yar uwa ce. Ko da kudi ko kyauta saurayi zai bada a lokacin, sai dai kawa ta amsa ta bada daga baya bayan saurayin ya wuce.

Daga karshe ta bayyana cewar cigaban da ake gani an samu ta anfani da wayar hannu ne ya kara kawo tabarbarewar tarbiya, tunda ta wannan hanyar ne yawanci samari da ‘yan matan ke aikawa da juna sakonnin sirri har su kaiga munafuntar juna.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG