Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakon Mu Na Yau, Ikram Rabi'u Mawakin Fina Finai Da Siyasa


Ikram Rabi'u
Ikram Rabi'u

A yau mun sami bakuncin Ikram Rabi'u mawakin fina-finai da kuma wakokin siyasa, Ikram ya ce yawan kallon fim ne ya sa shi sha'awar waka, inda ya rera wakarsa ta farko akan gwarzonsa wato Ali Nuhu.

Ikram ya bayyana cewa shi'awar wannan gwarzon nasa yasa shi'awar waka ta shiga zuciyar sa, kuma bai taba tunanin waka zata zamar masa sana'ar da zai dogara a kai ba sai da ya cigaba.

Mawakin ya ce a duk lokacin da yake rera waka, yana yi yana rausayawa domin hakan yana taimaka masa wajan rike baitukan wakar kamar yadda ya tsara su, kuma hakan yana taimaka masa wajan bin salon kidan domin a cewar sa idan kida da waka suka tafi dai dai, mai sauraro yafi nishadantuwa.

Daga karshe malam Ikram Rabi'u ya fadawa dandalin VOA cewar ya rerea wakoki da dama, kama daga wakar soyayya, siyasa da sauransu, kuma daya daga cikin wakokin sa wadda ta yi fice itace "darajar kwarya" wadda saboda ma'anar wakar aka yi ma film din lakabi da suna DARAJAR KWARYA.

A fannin tsegumi kuma, 'yan Kannywood da suka ziyarci birnin Los angeles na kasar Amurka domin yin wani kwas na sati uku sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja a yammacin jiya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG