Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bana Bakwai


Bana Bakwai
Bana Bakwai

A shirin mu na Bana Bakwai, Dandalin VOA ya sami zantawa ne da wasu matasa ‘yan mata da kuma wani saurayi inda suka fada mana irin nasu salon maganar!. Da farko dai sabuwar Kalmar tan nuna kora kiri kiri ba kunya misali idan kace wa mutum “KA WARE” ana warewa na nufin barin wurin cikin gaggawa.

Akwai kuma wata kalma kamar haka, “can ta matsemaka” wannan na nufin matsalar ka ce. Matashiyar ta bayyana hakan a matsayin yadda suke bayyana ra’ayi tsakanin juna.

Daga karshe dandalin VOA ya zanta da wani saurayi wanda yace idan mutum yana Magana kuma aka fahimci cewa karya yake, kuma ba’a son a nuna mashi cewar an san karya yake sai dai kawai a ce “Bugoshi” to duk wanda ke wurin zai gane cewar mutumin na fadar karya ne.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG