Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi: Daura Auren Dalibai A Makaranta Barazana Ce Ga Makomar Tarbiyya


Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi ta rufe wata makarantar Sakandiren Sa’adu Zungur dake jihar sakamakon zargin wasu daliban makarantar da aka yi da daurawa junansu aure a cikin aji.

Ta dalilin haka ne wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Abdulwahab Muhammad, ya sami jin tabakin wasu dalibai daga makarantar da kuma bangaren hukumomi domin jin tabbacin yadda lamarin ya kasance.

Wani daga cikin daliban makarantar ya bayyana cewar wasa ne kawai tsakanin dalibin da dalibar domin kuwa sun dauki lokaci suna tsokanar daliban da sunan saurayi da budurwa, wanda daya daga cikin abokan karatun nasu ya kawo alawa cikin wasa ya rarraba a ajin da cewar alawar daurin aure ce, amma a cewarsa duk wasa ne kawai.

Sai dai kuma mataimakin Gwamnan jihar Bauchi Architect Nuhu Gidado, ya bayyana cewa sun sami tabbacin afkuwar lamarin da sunayeb daliban, da waliyan da suka rarraba alawa da lemun bikin, harma da waliyan da suka amshi sadaki, lamarin da ya bayyana a matsayin babbar baraza ga tarbiya.

Domin Karin bayani, saurari rahoton Abduwahab Muhammad daga Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG