Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Kwanaki Uku Sama Da Mutane Miliyan 15 Suka Kalli Bidiyon


A faifan bidiyo da aka kafe a shafin yanar gizo na yahoo, wani mai goyon bayan dokar kare hakkin ‘yan kasa da hana mallakar makami a jihar Florida ta kasar Amurka ya yanyanka bindigarsa kirar AR15, a wani martani na nuna kin jinin harbi kan mai uwa da wabi da wani matashi ya yi a wata makarantar sakandire inda ya hallaka ‘yan makaranta goma sha bakwai.

Mutumin mai suna Scott Pappalardo, ya bayyana cewa bazai iya zama da tunanin cewa dan makwabcin sa zai iya daukar irin wannan makami ya fita waje ya dauki rayukan jama’a ba.

Da haka ya yi amfani da na’urar yanka karafa ya yanyanka bindigar tasa cikin ‘yan mintuna kalilan, kawo yanzu dai sama da Jama’a miliyan goma sha biyar sun kalli wanna hoton bidiyo da aka kafe a shafin facebook.

A cikin bidyon, Mr Papparlo ya bayyana cewa yana daga cikin masu goyon bayan kafa sabuwar dokar hana mallakar makami a Amurka, hatta ma zanen ta a jika da jama’a ke yi ya goyi bayan a haramta.

Mutumin ya kara da cewa jama’a da dama kan tambaye shi dalilin mallakar makami irin wannan domin kuwa babban makasudin mallakar babbar bindiga irin wannan shine domin aikata kisan kai.

An kafe wannan bidiyo ne kwanaki uku bayan matashin nan ya yi amfani da irin wannan bindiga kirar AR15, ya hallaka dalibai goma sha hudu da kuma malamansu guda uku, a makarantar gaba da firamare da ake kira Stoneman Doughlas High School, a jihar Florida dake Amurka.

Daga karshe ya yi bayanin cewa yana so ya kasance na farko da zai kawo sauyi ga al’umma, kuma duk da cewa jama’a da dama sun mallaki manyan makamai a gidajen su, lalata tasa da ya fara yi, ya nuna wa duniya cewa an sami raguwar akalla guda daya daga cikin dukan wadanda mutane suka mallaka.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG