Wani jirgin sama ya yi saukar gaggawa bayan wani fasinja ya yi ta sakin tusa yayin da suke cikin tafiya.
Wasu fassanjoji biyu ‘yan asalin kasar jamus dake zaune kusa da mutumin, sun fada masa ya daina tusa, amma yaki dainawa ya cigaba da sakin ta a jirgin Transavia, yayin da yake tafiya daga Dubai, zuwa Amsterdam Schiphole.
Ana zargin cewa ma’aikatan cikin jirgin basu taimaka wa fasanjojin dake zaune kusa da mutumin ba, suka yi korafi, jaridar Metro ta ruwaito cewa hakan ya sa fada ya kaure tsakanin fasanjojin amma duk da cewa direban yayi ta ja musu kunne, hakan bai hana fadan ba, lamarin da yasa jirgin ya chanza hanya zuwa filin saukar jiragen kasa na Vienna, inda jirgin yayi saukar gauggawa.
Bayan saukar jirgin sai ‘yan sanda biyu suka fitar da wasu mata biyu da maza biyu wadanda direban jirgin yace su suka jawo wannan fada a cewar jaridar Metro.
An saki fasanjojin su 4 daga hanun ‘yan sandan ba tare da an tuhume su ba, amma dai an haramta masu shiga jirgin saman Transavia na gaba.
Facebook Forum