Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tafiyar Awoyi Goma A Jirgin Sama Dan Yaro Ya Hana Fasinjoji Bacci Da Kukan Banza


Ba karamin ciwon kai bane kasancewa cikin jirgin sama har na tsawon awoyi takwas da dan karamin yaro yana ta tsuga ihu ya hana kowa shakatawa.

Fasinjojin sun kwatanta shi da jirgi daga jahannama wanda wani dan yaro mai shekaru uku da haihuwa ya yi ta kuka iyakacin karfin sa yayin da iyayen yaron suke cikin jirgin da ya taso daga kasar Jamus zuwa Amurka, kimanin tafiyar awoyi takwas ba kakkautawa.

Mahaifiyar yaron ta dimauce inda ta fara fadawa fasinjojin dake cikin jirgin cewa dan nata nada matsalar halaiya.

Wani daga cikin fasinjojin mai suna Shane Townly, ya bayyana cewa da alamu matar ta saba da kukan yaron, abinda kawai ya dame ta shine yadda jama’a suka kidime a sakamakon kuwwa da guje gujen da yaron ya yi ta yi.

Tun kafin jirgin ya bar kasar Jamus, wasu daga cikin fasinjojin sun ce sun ji lokacin da mahaifiyar yaron ta tambayi wasu daga cikin ma’aikatan jirgin su kunna yanar gizo domin yaron nata ya sami damar kunna kwamfutar sa ta hannu domin ya kalli hotunan wasanni na kananan yara.

A lokacin da ta fara Magana da ma’aikatan yaron ya fara daga murya sai ta fara bashi hakuri, a wannan lokacinne jama’a suka fara kallon juna domin sun san lallai akwai Magana.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG