A bayan da aka kammala zagayen farko na wasannin kwata fainal na cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, ya bayyana a fili cewa kungiyar Bayern Munich ta taka rawa wajen kashin da kungiyar Porto ta ba ta, a saboda kura-kuran ‘yan wasanta ne suka kai ga dukkan kwallaye uku da Porto ta jefa mata.
Kungiyar Bayern, wadda ta lashe wannan kofi a 2013, ta shiga filin wasa jiya a zaman wadda masana tamaula suke ganin cewa zata lashe wasan, amma kuma a wasu lamura na ban mamaki da suka faru a farko-farkon wasa, Ricardo Quaresma na Porto ya ci moriyar wasu manyan kura-kurai biyu da ‘yan Bayern suka tabka a minti 10 na farkon wasa. Da farko dai, ya buga fenariti cikin raga a bayan da dan wasan Bayern, Manuel Neuer ya kwashe dan wasan Porto, Jackson Martinez, a gaban gola.
Bayan wannan kuma, sai Quaresma ya kwace kwallo daga kafar Dante, yaje ya jefa ta salun alun a cikin raga, yayin da a can gefen fili, kwach na ‘yan Bayern Munich, Pep Guardiola, ya tsaya sai bude baki kawai yake yi yana ganin ikon Allah.
Kungiyar Bayern, wadda ta buga wasa ba tare da wasu shahararrun ‘yan wasanta irinsu Ribery ba, ta rama kwallo guda ta kafar Thiago Alcantara, jim kadan kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Amma da aka komo, Jerome Boateng na Bayern ya sake tabka wani kuskuren inda Martinez na Porto ya samu sukunin jefa kwallo na uku a raga.
Yanzu dai Bayern tana da namijin aiki a gabanta idan an zo zagaye na biyu a ranar talata mai zuwa.