Manajan kulub ‘din Chelsea Jose Mourinho ya fadi cewar bazai iya kamo ko zuwa dai dai da tsohon manajan Manchester United Alex Ferguson ba, wajen samun yawan zama zakaran wasan kalubalen turai wato Premier League, inda yake cewa wannan ba abu bane mai yiwuwa ba.
Manajan na Chelsea dai ya jagoranci kungiyar zuwa zama zakaran wasan ‘kalubalen turai da akayi ranar Lahadin da ta gabata, sun dai sami nasarar wasan da ci 1 – 0 a London da abokan karawar su Crystal Palace.
Wannan shine karo na uku da ‘dan shekaru 52 da haihuwa Mourinho ya zama zakaran turai, yanzu kuma yayi sanadiyar da kungiyar Chelsea ta kara zama zakaran turai biyon bayan zama da tayi a jere shekara ta 2005 da 2006.
Shi dai Alex Ferguson na da shekaru 51 a duniya lokacin daya jagoranci Manchester United ta zama zakaran wasan na turai, amma duk da haka Mourinho yayi watsi da maganar kamo Ferguson da yawan zama zakaran turai.
Inda yace, “ina da doguwar tafiya a gabana, amma Alex yayi abinda ba kowa bane zai iya yi. Bazan iya samun zama zakaran turai har sau 13 ba.”