Kungiyar Real Madrid, wadda ita ce zakarar kulob-kulob ta Turai mai ci yanzu haka, tana fuskantar jan aiki a gabanta, domin a karawar da zata yi asabar din nan da Sevilla, tilas ne ta yi kokarin samun nasara idan har tana son ta ci gaba da fatan lashe kofin gasar lig-lig ta Spain, la Liga.
Madrid tana bayan FC Barcelona da maki 2 a teburin La Liga, yayin da sauran wasanni 4 suka rage, amma aikin dake gabanta asabar shi ne, yau watanni 13 ke nan babu kungiyar da ta samu nasara a kan Sevilla a gidanta.
Haka kuma, Madrid zata yi tattaki zuwa wasan na asabar ne ana saura kwanaki 4 kacal kafin ta yi tattaki domin karawa da Juventus a wasan kusa da karshe na kofin zakarun kulob kulob na Turai.
Haka kuma, ita ma kungiyar Sevilla, ta matsu a kan lashe wasan da zata yi da Real Madrid domin tana gwagwarmaya da kungiyar Valencia wajen neman matsayi na 4 a teburin La Liga, watau matsayi na karshe da zai iya ba ta damar shiga gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai a shekara mai zuwa.
Kyaftin na ‘yan wasan Madrid, Iker Casillas yace wannan wasa na gobe, zai kasance mawuyaci kamar sauran wasannin da suka rage musu.