‘Dan wasan kungiyar Bayern Munich Jerome Boateng, yace dole ne kungiyarsa ta kara azama a wasan kusa da karshe da zatayi na Champion League ranar Laraba a gidan Barcelona, in ba haka ba karta damu kanta da zuwa Spain, biyo bayan sakacin da yayi sanadin fitar su daga gasar German Cup.
Burin kungiyar Bayern Munich dai shine ta mai mai ta zama zakarin wasan turai da suka samu yi a shekara ta 2013, a wannan kakar wasan dai ta karewa kungiyar ta Bayern bayan da kungiyar Borussia Dortmund fitar da ita daga gasar cin kofin German Cup a wasan kusa da karshe ranar Talatar, a buga kwallon daga kai sai gola.
Shan kashin dai ya biyo baya ne kwana biyu bayan lashe kofin Bundesliga.
Kungiyar dai tayi abin kirki da farkon wasan, inda kungiyar ta mamaye wasan har minti na 70, lokacin da kungiyar Dortmund ta fito da Henrikh Mkhitaryan ‘dan wasan ta na tsakiya komai ya canza.
Jerome Boateng dai yace kungiyar sa bata da wani zabi in banda yin wasa mai kyau alokacin da zasu ziyarci kungiyar Barcelona da take ba kanwar lasa ba a Spain.
Ya cigaba da cewa kungiyar Bercelona tana ‘daya daga cikin manyan kungiyoyi, idan har muka yi irin wasan da mukayi bayan minti 70 da Dortmund, to bashi da wani amfani a garemu muyi wasa da kungiyar Bercelona.