Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bin Ka’idoji Da Sharrudan Aikin Jarida


An Unidentified man reads a newspaper with headline Electoral Commission Chairman Attahiru Jega Apologies for elections postponement, published in Lagos, Nigeria, Sunday, April 3, 2011. Nigeria postponed its National Assembly elections Saturday as ballot
An Unidentified man reads a newspaper with headline Electoral Commission Chairman Attahiru Jega Apologies for elections postponement, published in Lagos, Nigeria, Sunday, April 3, 2011. Nigeria postponed its National Assembly elections Saturday as ballot

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, ta dukufa wajen janyo hankalin manema labaru da kafofin wasa labarai dabam dabam, domin bin ka’idoji da sharuddan aikin jarida, alokacin da za’a gudanar da zabe na kasa a cikin Najeriya.

Wannan tsarin da hukumar zabe ta dukufa wajen kokarin jawo hankalin manema labaru domin su gudanar da ayyukan su cikin ka’ida da dokokin aikin jarida, yazo ne alokacin da shugaban wallafa jaridu na daily trust mallam Kabiru Yusif, ya kaddamar da wani kundin littafi na dokokin aikin jaridu alokacin zabe, wanda ya sami hallartar shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega, da dukkan manya manyan editoci da masu kafofin wasa labarai daban daban, domin duba hanyoyi da za'a bi na ka’idojin jarida a kuma tabbatar da ba’ayi amfani da kafofin yada labarai ba wajen tada zaune tsaye.

A bayanin da mallam Kabiru Yusif yayi, yace za’a iya amfani da kafafen yada labarai na iya taimakawa wajen ingantar da zabe, ko kuma ya kawo cikas ga zaben, domin ta wannan hanya ana iya fadakarwa da nuna duk abinda ake ciki don jawo hankalin mutane ga abinda ya kamata da gargadi kan abubuwan da basu kamata ba.

XS
SM
MD
LG