Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyin Taimakawa Mutanen Da Rikicin Boko Haram Ya Afkawa


Majinyatta da suka jikatta kwance a asibiti a Kenya
Majinyatta da suka jikatta kwance a asibiti a Kenya

A satin daya gabata ne Farfesa Mohammed Kabir, kwararren masanin kiwon lafiya wanda ya goge a fannin kula da lafiyar jama’a na asibitin koyarwa na mallam Aminu Kano, ya fara yin mana bayanan matakan da za’a bi domin taimakawa mutanen dake cikin ‘dimuwa da kidima, a sanadiyar abubuwan keta da azabtarwa da suka gani a hare-haren ‘yan Boko Haram.

Farfesa yace, matakan da za’a bi guda takwas ne, na farko shine wadanda suka sami kan su cikin wannan hali, za’a kula dasu a asibiti na musammam in har an tabbatar sun shiga cikin halin damuwa da rudewar kwakwalwa, idan kuma ba’a sami asibiti ba a kusa sai a kawo likitoci da sauran ma’aikata wadanda suka kware a wannan aiki domin suyi musu magani.

Na biyu kuma shine kula da ayyukan rigakafi, musammam ga yara tunda akwai rigakafin ciwon tarin fuka, kyanda, foliyo harma da na titanos wanda ake baiwa ga manya ko matan da suke da ciki kafin su haihu. Hanya ta uku shine samar da muhalli, domin taimakawa wajen kwantar musu da hankali.

Sai kuma kula da tsaftar su domin kare su daga kamuwa da sauran cutattuka, dama kuma basu abinci mai gina jiki domin jikinsu ya samu karfin kare su daga daukar cutattuka. Halin zaman takewa, lallai a tabbatar da an samu ana kula da halin zamantakewar su da sauran ‘yan uwansu harma da sauran jama’a.

Ya kuma kamata wadanda suka sami kansu cikin wannan hali a koya musu sana’a’o’i, koda kuwa irin sana’ar kira, kafinta, dama saye da sayarwa, a kuma samar musu abinda zasu rike a hannun su domin baza ayi sana’a ba saida jari.

Hanya ta karshe shine tabbatarwa da cewa, zasu iya bin hakkin su kamar yadda dokar kasa ta basu, a kuma bi musu hakkin su ta gudanar da wadanda suka zaluncesu a shara’ance. Hakkin hukuma ne da jama’a dasu tabbatar sun bi wadannan hanyoyi domin taimakawa mutanen dake cikin ‘dimuwa da kidima, a sanadiyar abubuwan keta da azabtarwa da suka ganin a hare-haren ‘yan Boko Haram.

XS
SM
MD
LG