Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taimakon Likitoci Ga Yara Da Matasan Da Aka Kashewa Iyaye A Gaban Su


"Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.
"Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Hanyoyin da likitoci zasu iya taimakawa yara da matasa dama duk mutanen da suke cikin dimuwa a sanadiyar kashe kashen da suka gani da idanuwansu, daga ta’addancin maharan kungiyar Boko Haram. Munji ta bakin kwararren masanin kiwon lafiya wanda ya goge a fannin kula da lafiyar jama’a farfesa Muhammad Kabir, na asibitin koyarwa na mallam Aminu Kano, dake jihar Kano Najeriya.

Farfesa Muhammad yayi bayani inda yace kula da ire iren mutanen da suka shiga cikin wannan hali, suna bukatar wasu hanyoyi da ake bi domin samun daidaituwar rayuwar su alokacin da suka sami rashin daidaituwar hankali, wannan na kasancewa koda ta hanyar tabuwar kwakwalwa ko ta hanyar shiga wani hali mai sa tsananin damuwa, kamar yadda yara da matasan da suka shiga sanadiyar ganin yadda aka karkashe iyayensu da ‘yan uwansu.

Ga irin mutanen da irin wannan tashin hankalin ya rutsa dasu, suna samun matsala sosai a rayuwar su. Alamomin shiga cikin wani hali sanadiyar ganin irin wadannan tashe tashen hankula, shine mafarke mafarke, wasu kuma halayyarsu na canzawa wasu lokutan za’a gansu sun zauna bama sa cewa komai, wasu ma zasu rika yin surutai kamar su rika cewa sunga wani abu yana tahowa zai kamasu, da dai sauransu.

A kwai kwararrun dake da ilimin taimakawa ire iren wadannan mutanen da suka samu kansu cikin wannan hali, abubuwa biyu da ake kokarin samu shine daidaitawar muhallin mutane, da daidaitawar rayuwar mutane ta zama dai dai da duk abin da yake muhallinsa. Ana aikata wadannan ne don samun saukin al’amura da aka lura suna taba halayya don tabuwar aikin kwakwalwa ko kuma don shiga wani tashin hankali.

Karrama mutum na daya daga cikin hanyoyin da za’a bi domin taimakawa musu, kaisu gurin likitocin kwakwalwa domin samun kulawar da ta kamata, idan kuma ba’a samu zuwa asibiti ba to dole a kula da muhallin da mutanen suke domin yana taimakawa kwai da gaske.

XS
SM
MD
LG