Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Dan Iya Ya Gane A Kwai Rayuwa Bayan Zabe


Rayuwar Matasa A Life-Junction A Najeriya
Rayuwar Matasa A Life-Junction A Najeriya

Da yake ‘Dan Iya gwani ne wajen zaman dandali da tattaunawa, shiyasa daga ganina yace ‘dan uwa, bana fa akwai kaukawa, saboda tsakanin musulmi da kristocin kasar mu babu wata jituwa.

Haka nan tuni dangantaka tayi tsami tsakanin kudu da arewa, ‘yan siyasar kasar mu sun maida matasan mu kamar wasu ‘yan kokawa, burin su kullun kowanne ‘dan kasa yakoma bawa, shiyasa kawai suke ta kidan kadamu kamar wata garwa, idan kace yakamata a fahimci juna a zauna lafiya suce dakai ‘dan adawa, ni kuwa kullun na zauna tunani nake cewa bayan fa akwai wata rayuwa, kaga kenan dole ne mu fahimci juna tunda dai zaman tare ba makawa.

Nace eh ‘Dan Iya kaima kayi zurfin tunani, ni ma matasan kasar na bani mamaki tin tin tintuni, saboda dasu kullun ‘yan siyasa ke amfani kodai su jefa musu banbancin addini ko kuma su sassaka banbancin ‘kabila dana launi, saboda sudai babban burinsu kullun su kai ga wani tsani, da zasu tattakala su ‘dare ‘kokuwar gini ko wani tsauni idan yaso su sun tsira sai su barmu cikin tsanani, wani lokacin ma sai kaga tsakinmu ma harda zubar da jini, kaga kuwa wannan shine ke kawo mana matsala a kowanne fanni.

‘Dan Iya yace eh gaskiya naji dadin wannan magana amma ta yaya sauran ‘yan kasa zasu amfana? Nace to ‘Dan Iya babban batun dai shine dole duk abinda zamuyi mu zauna, idan muna da wata matsala sai mu tattauna, a karshe kowa ya kawo shawararshi a auna, saboda idan har muna son gujewa dukkan futuna tare da tabbatar da samar da zaman lumana, to dole mu tsara zara zaren tsirku da tsananin tsana.

A maimakon haka ma kullun mu rinka rikewa juna amana ta hanyar gujewa ‘yan siyasar dake mana juyin waina. ‘Dan Iya yace to yanzu dai wannan tattaunawa tamu tasa na gane akwai rayuwa bayan zabe, saboda haka babu dalilin barin alaka ta da sauran mabiya addinai ko ‘kabilu ta cabe, maimakon haka ma zan kyautata dangantakar mu ne tunda akace da sabon gini gwanda yabe, saboda kar ‘dan zaman lafiyar da muke morewa ya sullube, harma takai da gudun tsirar tserewar tsaka tsamin tsunbula kuwar tsaron da muka tsinci kai a ciki ta rafka tuntube.

XS
SM
MD
LG