Kulob din Flying Eagles na ‘yan kasa da shekaru 20 na Najeriya ya lallasa takwaran sa na Ghana da ci 2 – 0 ranar larabar nan a karawar su ta kaiwa karshen gasar kwallon kafar Afirka ta ‘yan kasa da shekaru 20 da ake yi a Senegal.
Da farkon wasan dai ‘yan wasan na Ghana sun kame filin inda suka hana ‘yan wasan na flying eagles walwala, amma duk da haka ‘yan wasan na Flying Eagle suka auna kwallon su ta fari a raga cikin mintuna 23 na wasan.
Dan wasan Flying Eagles Captain Musa Muhammed ne ya dauko wani bugun kwana mai kyau, sannan Obinna Nwobodo kuma ya gyara ta da kai wanda ya sauya yanayin wasan.
Najeriya ta zo daf da jefa kwallon ta ta biyu, amma wani yunkuri da ‘yan tsaron gidan Black Satallites na Ghana suka yi yasa hakan yaci tura.
Duk da haka ‘yan wasan na Ghana basu daina kai kora ba, yayin da cikin rabin awa, Yaw Yeboah yayi wani bugun kwana mai matukar kyau amma dan tsaron gidan Najeriya Joshua Enaholo ya kabe ta gefe guda.