Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Liverpool Na Cigaba Da Samun Nasara


Manchester City's Samir Nasri (L) gestures to Liverpool's Jordan Henderson during their English League Cup semi-final, first leg soccer match at the Etihad Stadium in Manchester, northern England, January 11, 2012.
Manchester City's Samir Nasri (L) gestures to Liverpool's Jordan Henderson during their English League Cup semi-final, first leg soccer match at the Etihad Stadium in Manchester, northern England, January 11, 2012.

Ba karamar kadara ta sa yan wasan kulub din Liverpool, kai wa ga fafutukar neman shiga gasar champion league jiya litinin ba, a daya bangaren kuma ta sami nasarar zuwa wasan kusa dana karshe na cin kofin kalubale kungiyoyi FA, wanda rabonta da tazo wannan matsayi tun alif 1927.

‘Dan wasa Jordan Henderson, ne ya sami sa’ar zarga kwallo a raga a cikin mintuna sittin da takwas, hakan ne ya baiwa klub din Liverpool damar lashe wasan data buga da Swansea ‘da ci daya da babu, a gasar premier league. Henderson dai ya zarga kwallo daga nesa inda ya buga ta damar wani dan wasan tsakiyar Swansea kwallon dai ta kai ga kusurwar raga.

Bayan gama wasanne Hederson yace, “na samu sa’a saka kwallon cikin raga, amma samun irin wannan nasara, dole sai kana gurin daya dace kafin ka sami cin kwallon.

Liverpool din dai ta cigaba da samun nasara a wasannin ta wanda har yanzu babu wata kungiya data samu nasara akan ta cikin wasannin da buga a baya har goma sha uku, tun daga ranar sha hudu ga watan Disamba, a yanzu haka dai tana bayan kungiyar Manchester United da maki biyu, ita dai Manchester tana da maki hudu, kuma tana gurbin karshe na masu shiga gasar Champion league. Abokan hamayyar biyu dai zasu kece raini a fagen wasa ranar lahadi, idan Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG