Kwamitin lafiya na UEFA ya amince da wani sabon tsari na gwajin fitsari na lokaci mai tsawo , baya ga tsarin gwajin jinni wanda ake amfani da shi a yanzu domin bin diddigin yanayin jikin ‘yan wasa.
Duk dan wasan da aka yiwa gwaji a kulob din UEFA da kuma masu shiga gasa na da wasu alamomi a jiki wadanda a takaice ke nuna illar shan kwayar kara kuzari wanda hakan ke taimakawa wajan inda za a bada karfi wajan gwajin, a cewar hukumar kwallon kafa ta turai.
A shekara ta 2013 UEFA ta fara amince wa da gwajin fitsari inda aka gwada na ‘yan wasa har guda 900 domin binciken hanyar da za a bi wajan gano muhimmiyar hanyar tantance masu anfani da kwayoyin kara kuzari. Amma har yanzu ba’a fitar da sakamakon wannan binciken ba.
Koda shike wasu kadan daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa sun taba samin matsalar anfani da kwayar kara kuzari har ma UEFA ta dakatar da wasu ‘yan wasan kasar Rasha su uku a shera ta 2009 – 10.