Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Rikicin Boko Haram Yafi Shafa


A tambayar da mukayi wa masu sauraran mu, kan wa suke gani a ra’ayinsu rikicin ‘yan Boko Haram, yafi shafa tsakanin matasa da yara kanan, mun sami ra’ayoyin masu sauraro da dama kan wannan tambaya, kuma ga kadan daga cikin su.

Adamu Aliyu Ingulde yace, shi dai anashi harsashen, wannan rikici na ‘yan bindiga ya fi shafar shafar matasa ne, saboda akalla ni da abokai na mun kai goma da muka kammala karatun sakadare a garin Dambuwa, amma yau an wayi gari kusan mutum shida daga ciki an kashesu, duk a dalilai na rikicin ‘yan bindiga.

Ita kuma Hadiza Adamu, na ganin Mata ne suka fi shan wuya, dama yawancin matan Arewa basu saba neman abinci ba, to sai gashi an kashe mazajensu an barsu da yara kanana, sune da neman abinci, sutura, duk nauyin gida ya dawo kansu ga wahalar gudu a jeji, wasu kuma an barsu da juna biyu hasbunallahu wa ni'mal-wakil.

Mata an kashe musu mazaje, anyi musu fyade, anyi ma ‘diyansu, an kuma barsu da yara a yankin da aka tsiyata, sako daga Yahaya Yusif. Shi kuma yusif Isa, na ganin matasa sun fi don sojoji basu kashe kananan yara da mata.

Ai wallahi ta’addancin ‘yan Boko Haram, anan Arewacin Nigeriya babu wanda bai shafa ba, maza, mata, matasa, yara, tsofaffi har dabbobin mu na Arewa, kai wallahi har bishiyoyin mu na Arewar Najeriya sun san ana tafka ta’addanci, Allah ka rugugguza duk wani azzalumi ‘dan ta’adda mace ko namiji, yaro ko babba sako daga Abubakar Mohammed.

Saurari sauran ra’ayoyin cikin sauti.

XS
SM
MD
LG