Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Akan Masu Cin Amana Aure


A kwai jama'a da dama wadan da yawancin lokaci kan ci amanar mata ko mazan su, ba tare da sun gane ba. abin da ya kamata mutane masu irin wannan halin su sani shine, baza ka taba gane irin azancin da mutane ke da shi ba musamman idan ran su ya baci musamman idan aka ci amanar su.

Gaskiyar dai ita ce baza a iya bada yawan adadin maza da mata manya da matasan da ke boyewa bayan wani dalili sa'annan su yi ta cin amanar matan su ko mazan su ba.

Babu wani takamaiman dalilin hakan da ke da nasaba da yanayin dan adam, koda shike abin yana konawa duk wanda, ko wadda saurayinta ko matar sa suka sami kawunansu a cikin irin wannan hali matuka.

Kamar yaddad wani bincike da aka gudanar a shekarar 2015 a kasar Ingila, ya nuna cewar maza sun fi mata saurin gane idan matan su sun ci amanar su cikin sauri fiye da mata. wannan tamkar wata baiwa ce da aka gano cewa tana tattare a cikin hallitar maza.

Binciken ya bayyana cewa yawancin masu cin amanar misalin kashi 60% cikin dari sukan dauki shekaru kamar biyar suna cin amanar. haka kuma kashi 18% kan fara kuma su bari ne a cikin shekara guda. sai kuma kashi 12% cikin dari wadanda sababbin aure ne.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG