Cibiyar nazari da bincike akan Tsirrai da kayan lambu ta Najeriya ta kirkiro fasahar kashe kwari masu yada kwayayen dake rikidewa su zama tsutsar dake lalata gonar Tumatur wacce ake yiwa lakabi da Ebolar Tumatir.
A shekara ta 2015, aka fara samun rahotan bullar kwarin a wasu jihohin Najeriya, amma a shekara ta 2016 da ta gabata, kwarin sun haddasawa manoman Tumatur asarar dubban miliyoyin Naira, musamman a jihohin Kano da Kaduna da Katsina da kuma jihar Gombe.
Lamarin ya karya daruruwan manoma musamman bisa la’akari da yadda wadannan kwari ke yada wannan tsutsa mai hallaka Tumatur a gona ke bijirewa duk wani nau’in maganin da manoman suka fesa domin kashe su.
Annobar ta zaburar da kwararru a cibiyar nazari da bincike kan tsirrai da kayan lambu ta Najeriya mai shelkwata a birnin Badum, wajan kirkiro fasahar da zata taimaka wajan kawar da wannan annoba.
Malan Habu Sale Hamisu, babban jami’i ne a ofishin shiyya na cibiyar dake Bagauda, a jihar Kano, ya bayyana cewa da suka gudanar da bincike kuma suka sami nasarar gano jihohin dake fama da annobar, sun rika zuwa jihohin suna kamo kwarin inda suka shiga bincike domin samo dabarar hallaka wannan kwaro da baya jin magani.
Malam Habu, ya kara da cewa sun yi gwajin sabuwar dabarar a gonakin tumatur da dama dake a dukkan jihohin da sukai fama da annobar. Tuni manoman Tumatur suka fara bayyana farin cikinsu kan wannan sabuwar fasaha ta hallaka kwarin da ke haifar da cutar Ebolar Tumatur.
Daga Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana da rahoto.