Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibi A Afirka Ta Kudu Ya Saci Mota Don Zuwa Zana Jarabawar Karshe


A statue of British colonialist Cecil John Rhodes at the University of Cape Town near the city centre of Cape Town, South Africa, March 17, 2015.
A statue of British colonialist Cecil John Rhodes at the University of Cape Town near the city centre of Cape Town, South Africa, March 17, 2015.

Kafafan yada labaran Afirka ta Kudu sunce wani ‘dalibi ya saci motar bus alokacin da yake kokarin zuwa ‘daukar jarabawar lissafi ta karshen shekara.

Gidan jaridar eNCA ne ya fitar da rahotan a jiya Alhamis, inda yace ‘dalibin mai suna Le-Aan Adonis ya tuka motar ne bayan shi da sauran ‘daliban suka jira direban motar amma bai zo ba.

Matashin dai yace ya samu motar da ‘dan mukullinta ciki, inda sauran daliban suka tambayi matashin mai shekaru 20 da haihuwa da ya tukasu, kasancewar sun yi imanin zai iya kai su inda zasu je lafiya.

Cikin tafiyar ne jami’in kula da zirga zirgar motoci ya tsayar da su a wani kauye kusa da makarantar su, dake yankin Cape, ya kuma rubuta tarar kimanin Naira dubu 70 ga matashin.

Bayan haka kuma Adonis zai fuskanci tuhuma daga hukumar makaranta, wanda yanzu haka ya sami lauyoyi na kokarin kare shi kyauta, har ma da nema masa kudaden da zai biya tarar.

XS
SM
MD
LG