WASHINGTON, DC —
Shahararren dan wasan barkwanci na Hausa, Rabilu Musa, wanda aka fi sani da sunan Dan Ibro, yace yana nan daram da ransa kuma da lafiyarsa, sannan kuma duk jita-jitar da ake yadawa cewa ya mutu, to albishir ne na abubuwan alkahiri dake samunsa.
Rabilu Musa ya fadawa Dandalin VOA a cikin wata hira ta musamman cewa shi kam yanzu ma aka fara damawa da shi, domin harkokinsa ba su taba bunkasa kamar yadda suke yi a yanzu ba.
Dan Ibro ya gode tare da yabawa magoya baya da masoyansa wadanda suka yi ta kiransa a waya ko aikewa da sakonni domin jajen wannan abu da ya samo asali daga wasu shafuka na intanet.
A shekarun baya ma, an yi ta yada jita-jitar rasuwar Dan Ibro har sai da ya fito da bakinsa ya karyata wannan a cikin filin A Bari ya Huce.
Ga cikakkiyar hirar ta baya-bayan nan da Dan Ibro.