WASHINGTON, DC —
NAJERIYA - Wani masani kan harkokin tsaro mai Hussaini Monguno, ya bukaci hukumomin tsaron Najeriya da su fito su fadawa duniya gaskiyar abinda ya faru a hedkwatar hukumar tsaron SSS a karshen mako. Shi kuma manjo Yahaya Shinku mai ritaya, cewa yayi idan har abinda hukumar SSS ta fada gaskiya ne, to akwai sakaci babba.
NAJERIYA - Shahararren dan wasan barkwanci na Hausa, Rabilu Musa, wanda aka fi sani da sunan Dan Ibro, yace yana nan daram dinsa, a bayan da wasu suka sake yada jita-jitar cewa ya mutu. A shekarun baya ma, wasu jama’a sun yi ta yada jita-jitar cewa dan Ibro ya rasu.
NIJAR - ‘Yan majalisun dokokin jam'iyyun adawar Nijar sun dauki matakin maida martani kan abinda suka kira kin biyayya ga dokokin kasa da mahukumtan kasar suke yi. A husace 'yan majalisar sun dauki matakin kin yin magana a duk lokacin da majalisar ta nuna bukatar gayyatar wani minista daga cikin ministoci wadanda membobi ne na jam'iyyun adawa da suka shiga cikin gwamnati ake damawa da su a cikin gwamnati da sunan jam'iyyun adawar.
SOMALIYA - Gwamnatin Somaliya ta ce ta damke wasu manyan kwamandojin sojan kungiyar al-Shabab su biyu, daya daga cikinsu wanda ake zargin yana da hannu a harin bam da ya kashe mutane fiye da 20. Jami’ai sun nunawa ‘yan jarida mutanen biyu yau talata a garin Qoryoley, amma ba su bayyana sunayensu ba, su na cewa sai an kara gudanar da bincike. Mukaddashin ministan tsaro, Ibrahim Isak Yarow, ya fadawa VOA cewa ana zargin daya daga cikin mutanen da hannu a harin kunar bakin wake da aka kai kan sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na KTKA a watan satumbar 2009 a Mogadishu.