WASHINGTON, DC —
IWani dan majalisar dokokin jihar Borno, Mohammed Sale Banga, mai wakiltar mazabar Kwaya-Kusar, yace da mamaki yadda aka shige da daruruwan mata cikin dajin dake kewayen Chibok ba tare da jami'an tsaro sun sani ba.
Dan majalisar yayi tambaya, yana cewa, "shin ko doka aka ba su cewa dajin nan kada a shige ta sai an tafi da wadannan yaran?"
Mohammed Sale Banga, yace "ina jin cewa ana ce jeji-jeji. Jejin nan fa akwai garuruwa duk a ciki. Jejin nan ina jin duk wadanda suke yankin in aka ce Gwoza sun san iyakacin jejin Gwoza, wadanda suke yankin Damboa sun san iyakacin jejin Damboa, wadanda suke yankin Chibok inda wannan abin ya faru sun san iyakacin jejinsu, ba inda ba a sani ba."
"Kuma azo a ce a cikin jejin nan ba a san inda ‘yan matan nan suke ba, shin jami’an tsaron nan, duk da kokarin da suke yi yadda muke ganinsu a nan jihar Borno, shin doka aka ba su ne cewa jejin nan kada a shige ta sai an tafi da wadannan yaran?"
Ana iya sauraren cikakkiyar hirarsa a nan kasa