WASHINGTON, DC —
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya umurci manyan jami'an tsaro na kasar da su dauki duk wani matakin da zasu iya na ganin an maido da dalibai mata su fiye da 200 da tsagera suka sace a watan da ya shige daga wata makaranta.
kakakin shugaban, Reuben Abati, yace Mr. Jonathan ya bayarda wannan umurni yau lahadi, a bayan da ya gana cikin sirri da hafsoshin rundunonin sojan kasar, da manyan jami'ai da kuma shugabar makarantar da aka sace wadannan dalibai.
Abati yace shugaban ya bayar da umurni a fili cewa "tilas a dauki dukkan matakin da za a iya na tabbatar da cewa an maido da daliban nan lafiya."