Rikici tsakanin direbobin manayn motoci da sojoji ya haifar da dogayen layukan manyan motoci a hanyar zuwa babbar tashar jiragen ruwan najeriya na apapa.
Direbobin na zargin sojojin da yansanda na karban na goro da kuma gallaza masu ta hanyar gwale gwale idan har suka kasa basu abin hasafi, wakilin sashin Hausa Babangida jibrin yaje gurin da ake wannan rikici.
A cewar daya daga cikin direbobin da jami’an tsaron suka tsayar, sun nemi ya basu na goro, shi kuma ya basu naira dari biyu amma sai suka ce naira dubu akae bada wa.
Ya kara da cewa, “sun umurce ni da in fito daga mota amma na ki yarda, sai suka sa wuka suka fasa mani tayar mota, da kuma farfasa dukkan maduban motar. Wani daga cikin su ma sai da yayi harbi a iska domin dai kawai suna so su razana mu.”
Direban ya bayyan cewa sai da daya daga cikin manyan sojojin yazo yace ya fito daga mota sa’annan ya fito, kuma sai babban sojan ya sa shi yayi ta birgima a kasa, yaron motar sa kuma na fitowa sai suka kama shi da bugu har suka jefa shi cikin ruwa inda ya suma.
Yanzu haka dai rahotanni sun nuna cewa yaron motar na asibiti rai hannun Allah, direbobin kuma suna nan sun tare hanyoyin da cewar sai an biya su gilasai da tayar da jami’an suka bata masu.