Mai horar da ‘yan wasan kasar Swaziland, Harris Bulungu, ya ce canje-canjen da takwaran aikinsa na Najeriya Sunday Oliseh ya yi ne, ya birkita masa lissafi ya kuma basu nasara.
‘Yan wasan Super Eagles sun lallasa na Swaziland ne da ci 2-0 a jiya Talata a filin wasan garin Fatakwal.
Wannan nasara kuma ta basu damar shiga zagaye na gaba a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2018.
A cewar Bulungu, Oliseh ya mamaye shi, da ya ajiye John Mikel Obi da Godfrey Oboabona da Elderson Echiejile a farkon wasa, a maimakon haka ya saka Chima Akas da Austin Oboroakpo.
Bulungu ya kara da cewa wasan da Super Eagle ta buga ya fi wanda suka kara a farko domin suna da ‘yan wasan tsakiya masu kuzari.
A cewarsa, sun so su yi amfani da damar da suka gani a wasan farko ganin yadda Najeriya ta yi wasa babu kuzari a Lobamba, amma sai Oliseh ya sauya yanayin ‘yan wasansa a wannan karo, lamarin da ya dagula musu lissafi.