WASHINGTON, DC —
Mai kula da ‘yan wasan Super Eagles, Sunday Oliseh, ya ce akwai babban kalubale a gaban su domin rukunin da suke cikin ba kanwar lasa bane.
Super Eagles dai na rukunin C ne inda aka hada su da kasashen Tunisia, Guinea da Niger, a gasar cin kofin nahiyyar Afirka.
Najeriya ta samu damar shiga gasar ne baya da ta doke kasar Burkina Faso da ci 2 da babu.
Koch Sunday Oliseh, yana mai cewa duk kasashen da suka samu hayewa gasar da za’a fara ranar 16, ga watan Janairu 2016, suna da zaratan ‘yan wasa, wanda yake nufin tilas ne su zage damtse.
Ya kara da cewa su kam zasu far shiri ne bayan garawar da zasu yi yau da kasar Swaziland.