Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaima Ka Yi Dariya


Wani bahillatni ne ya shiga motar haya zuwa wani gari, ana cikin tafiya sai jama’a suka fara gyangyandi a mota kamar yadda dai aka saba.

Ana cikin tafiyar sai Karen mota ya fara amsar kudin mota, kamar yadda ake yi bisa al’ada Karen mota yakan tambayi kowane fasinja inda zashi sa’annan ya fada mai kudin da zai biya.

Da aka zo kan bahillace sai Karen motan nan ya ce malam ina zauwa? Ashe shi kuma bahillace ya manta da sunan inda zashi!

Koda ya waiga sai yaga wani daga cikin fasinjojin na ta sheka bacci da baki a bude, sai bahillacen nan ya ce garin da zani ya yi kama da bakin wanncan sais hi kuma Karen mota y ace kacako zaka?

Sai malamin ka ya amsa yauwa kacako zani!

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG