A safiyar yau ne aka sami labarin sace mahaifiyar kociyan kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shakaru 23, Mr. Samson Siasia. Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga ne suka shiga gidan mahaifan nasa, safiyar yau Talata a unguwar Odoni da ke karamar hukumar Sagama ta jihar Bayelsa, kuma suka tafi da ita a bisa babur.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ASP Ansinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa an sanar da su da batun amma babu wani cikakken bayani.
Da ya ke Magana da ‘yan jarida, Siasia ya bayyana irin halin damuwar da ya ke ciki bisa ga abinda ya faru, ya ce “yanzu ni kam a rikice nake. Bisa ga labarin da na samu, wasu maza guda 3 ne suka shiga gidan mahaifana a kauyenmu na Odoni, su ka haharba harsasai a iska kafin suka tusa keyar mahaifiyata suka tafi da ita bisa babur.
Ya cigaba da cewa” me suke bukata daga gareni? Bana da kudi, yanzu haka ina yi wa kasata aiki, kuma ina bukatar natsuwa don ganin ‘yan kungiyar kwallon kafar ta ‘yan kasa da shekaru 23 sun sami nasarar wasan da za su yi don su sami zuwa wasan Rio. Don haka ina rokon su da su taimaka su kyaleta.
A wata sanarwa da aka fidda daga shafin hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF), shugaban hukumar Amaju Pinnick ya roki wadanda suka sace mahafiyar kociyan, ‘yar shekaru 72 da haihuwa da su sake ta. Ya ce wannan abun tashin hankali ne matuka. Muna kan shirin muhimmin wasan da zai sa mu sami nasarar zuwa kwallon kafa ta duniya da za a yi a shekarar 2018, kuma yanzu haka ‘yan wasan na Gambiya don shiri.