Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Wani Kwarto Ta Cika A Ajegunle


A wata unguwa da aka fi sani da Ajegunle da ke jahar Legas, wani mutum mai suna Udoh ya kama matar sa dumu dumu tana a kan gadon sa tare da wani makwafcin sa.

Rahotanni sun bayyana cewar matar mutumin mai suna Gift, tana yara biyu da mijin nata, shi kuma makwabcin mai suna Chukwuka suna cikin kwana da juna ne a yayin da mr Udoh wato mai gidan nata ya dawo inda sauran makwabtan suka bashi labarin abin da ke faruwa.

An bayyana cewa Mr Udoh ya leka dakin sa da ke rufe ta wata 'yar kofa sai kwatsam ya kamasu akan gadon sa suna kwana da juna. Wani daga cikin makwabtan mai suna Joseph ya bayyana cewa Mr Udoh ya tafka kuwwa ya kira sunnan matar sa da karfin gaske, ita kuma ta yi maza maza ta bude kofa inda gogan naka ya afka cikin dakin da gudu.

A yayin da ya shiga dakin, wadanda aka yi abin agaban su sun bayyana cewar sunga lokacin da Mr Chukwuka ya daka tsalle ya fita ta wata kofa da ke baya a guje daga dakin kuma ya tsere fintikau.

Shaidun sun ce lokacin da Mr Udoh ya fito waje rike da adda, da matar da saurayin nata sun ranta cikin na kare. Mr Udoh ya saha alwashin cewar idan daya daga cikin su ya yi kuskuren dawowa gidan lallai zai yi masa gunduwa gunduwa da addar sa.

Sun kuma kara da cewa mutumin ya kira yayan matar tasa inda ya umurce shi da ya fada mata cewar ta kwashe kayan ta tabar masa gida kokuma saidai su zo su dauki gawar ta.

Makwabtan dai sun dade suna ganin Mr Chukwuka na aikata irin wannan hali a unguwar da yake zama da matarsa da kuma sauran iyalinsa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG