Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Kungiyar Kamfanonin Sadarwa Ta Matasa


Ogbonnaya Bassey ya samu shiga gasar matasa masu fasaha da kungiyar hadakar hanyoyin sadarwa na zamani ta shirya yi wannan shekarar ITU Telecom World 2015.

Wannan gasar da kungiyar ta shirya wata hanya ce ta shiga fadin duniya domin zabo matasa masu basira da fasaha, domin neman hanyar da za a bi wajen samun cigaba da kawar da kaluben da ke addabar wannan zamani. Shirin dai ya na hada manya-manya shugabanin duniya da fitattun ‘yan kasuwa da masu kamfanoni.

An zabi matasan da zasu shiga wannan gasa cikin mutane 124 daga kasashe daban-daban har 34 dake fadin duniyar nan, Ogbonnaya Bassey dai zai halarci wannan taron da zai fara ranar litinin 12 ga watan Oktoba zuwa Alhamis 15 ga wata, a birnin Budapest da ke kasar Hungry.

Basirar da ta sa Bassey ya samu shiga wannan gasa kuwa ita ce, yadda za a samar da fasahar yin amfani da hasken rana wajen samar wutar lantarki cikin rangwamen farashi, ga masu amfani da injin din janareto a fadin duniya, kasancewar rashin wutar lantarki da wasu kasashe ke fama.

Fasahar dai za ta taimaka wa masu kananan sana’o’i da masu gidaje wajen biyan kudaden da basu ta ka kara sun karya ba. Akwai kyautuka masu tsoka ga duk wanda ya samu nasarar wannan gasa, da samun damar juya mafarki ya zamanto gaskiya.

XS
SM
MD
LG