Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Mai Jiran Gado a Shirye Yake ya Dauki Matakin da ya Dace


Gwamnan jihar Neja, mai jiran gado Abubakar sani Bello, ya bayyana damuwasa akan yadda bala’in gubar dalma ta hallaka yara ashirin da takwas a jihar.

A makon jiya ne dai jami’an kiwon lafiya suka bayyana bullar cutar a yankin karamar hukumar Rafi, dake jihar ta Neja.

Alhaji Abubakar Sani Bello, ya shedawa manema labarai cewa lamarin nada matukar tayar da hankali musamman ganin yadda abun ya shafiyara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar.

Ya kara da cewa a shirye yake ya dauki duk matakin da ya dace na shawo kan lamarin da zaran ya karbi ragamar mulkin jihar.

XS
SM
MD
LG