Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hattara Dai Masu Shafukan Sadarwa Na Instagram


Instagram
Instagram

A cewar kamfanin da ke kula da harkokin tsaro a janar gizo Symantec, yace a kafar sadarwa ta Instagram ana yiwa shafukan mutane kutse, kuma a cika su taf da hotunan batsa, domin ja hankulan mutane zuwa ga wasu shafukan yanar gizo na batsa.

Duk shafin da aka yiwa kutse yawanci akan canza hotan mutum zuwa na wata macen da bata sanye da kaya jikin ta, kuma babu ruwansu da cewa mace ce ko namiji ne ya mallaki shafin, a cewar rahotan kamfanin tsaro a yanar gizo kan shafin sadarwa na Instagram.

A yayin da yake bayani kan shafukan da aka yiwa kutse, Symantec, yace ya gano cewa ana canza sunan da mutum ke amfani da shi zuwa wani suna na daban, ana kuma canza bayanan mutum baki daya zuwa wani na daban, a kuma cika shafin da hotuna.

A cewar kamfanin, a kan umarci mutum da ya danna wani adireshi, wanda da zarar mutum ya danna zai dauke shi zuwa shafin yanar gizo na batsa. Duk da hotunan da masu kutsen ke karawa a shafin da suka kwace ikonsa, sukan bar hotunan mai shafin ba tare da sun goge ba.

Haka kuma masu kutsen kan canzawa mutane password dinsu, ta haka ne kuma mutane kan gane cewa anyi musu kutse. Ko bayan wasu watanni shafin zai kasance kamar yadda yake, wanda ke nuna alamun mai shafin ya sake bude wani sabon shafin, inji Symantec.

Kamfanin na ganin ire iren wannan kutse na faruwa a dalilin rashin amfani da password mai karfi. Kamar yadda yace “yayin da bamu da masaniyar yadda shafukan kan fada hannun masu kutsen, muna dai zaigin yin amfani da password maras karfi da yawan yin amfani da password ‘daya suken ke janyowa, musamman ma tunda sama da password Miliyan 600 ne ke yawo cikin wannan shekara bayan da aka bankado su a wasu shafuka da akayiwa kutse.

Symantec ya shawarci masu amfani da shafin sadarwa na Instagram da suyi amfani da sabon tsarin da Instagram ya fara fitarwa domin kare kansu.

Sabon tsarin kuwa shine kirkirar wata manhaja kariya da za ta kare masu kutse daga karbar ikon shafin mutane. Duk da haka dai, ba duk masu shafukan Instagram ne ke da wannan manhaja ba tukunna. Amma mutane zasu iya dubawa su gani ko suna da ita a shafukansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

XS
SM
MD
LG