‘Yan sanda sunce sun kama mutumin nan da ake zargi da shiga ‘dakin karatu yana makalewa karkashin teburi yana shinshina kafar mata ‘dalibai.
Jami’an tsaron dai sunce sun cafke wannan mutumi ranar talata, mutumin mai suna Eddy Juan mai shekaru 52 ya shiga hannun jami’an ranar Talata, inda ake tuhumar sa da laifukan masu yawa.
Bada dadewa ba ‘yan sanda suka fitar da wata takardar sanarwa suna gargadin ‘dalibai cewar an ga wani mutum ranar 29 ga watan Agusta, karkashin kujera a ‘dakin karatu yana shinshina kafa, har ma sun fitar da kamannin mutumin.
Daga baya ne jami’an suka sami wani mutumi mai kama da wanda ake zargi kan ‘dan karamin babur, ‘yan sanda sunyi kokarin tsayar da shi domin tambaya amma mutumin ya ruga, har sai da yayi hatsari kafin ya tsaya.
Haka ne yasa ya karawa kansa laifi, ba’a dai fadi halin da ake ciki ba ko za’a iya sakinsa kan beli, babu kuma tabbacin cewa mutumin yana da lauyan da zai kareshi.