Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Sabon Bincike Akan Cizon Sauro


Malaria
Malaria

Sakamakon binciken wanda aka wallafa shi a wata mujalla mai suna “Malaria Journal” a turance, ya yi dubi ne kan inda aka gina wasu madatsun ruwa dubu 1,270, wadanda ya alakanta da matsalar zazzabin cizon sauro.

Ya kuma gano cewa fiye da mutane miliyan daya a kasashen Kudu da Hamada, za su kamu da cutar Malaria a wannan shekara saboda suna zaune a kusa da wadannan dam.

Mathew McCartney, na cibiyar da ke lura da yadda ake sarrafa ruwa a kasashen duniya, shi ne ya jagoranci wannan bincike.

Ya ce mun gano cewa zama a kusa dam na da alaka da kamuwa da cutar malaria, saboda wurin yana zama matattarar da sauro kan kyankyashe kwansa, musamman ma a gabar madatsun ruwan, saboda haka yawan sauro ya kan karu sosai a irin wadannan wurare.

Wannan bincike dai ya yi dubi ne kan wasu madatsun ruwa 78 da ake shirin ginawa a wasu kasashen Afrika.

Akwai ayyukan da ake yi na bunkasa fannonin tattalin arzikin kasashen da ke Kudu da Hamada, kuma mafi yawansu sun ta’allaka ne wajen gina sabbin dam.

Idan kuma har aka kammala gine-ginen dam din, lallai za a samu karin wadananda za su kamu da cutar zazzabin cizon sauro, wadanda adadinsu zai iya karuwa zuwa dubu 56 a duk shekara. Sai dai McCartney ya ce akwai bukatar a saka shirin kawar da barazanar da Malaria ke haifarwa, cikin ayyukan ci gaban da ake shirin tunkara.

Saboda haka muna kalubalantar masu ruwa da tsaki a wannan harka da suka hada da masu tsare-tsare da hukumomin da ke samar da ruwan sha, da su san cewa ayyukan da sukan yi, kan haifar da matsaloli kamar na cutar malaria, kuma akwai bukatar su dauki matakan magance su.

Akwai hanyoyin da a za iya magance wannan matsala ciki har da na gargajiya, kamar yin amfani da gidan sauro da magungunan feshi, za kuma a iya daidaita yawan ruwan, wanda hakan zai taimaka wajen kashe koyin sauron, sannan har ila yau, yin amfani da kifaye zai taimaka wajen cinye kwayayen sauron.

Sai dai sakamakon wannan bincike bai gaza wajen nuna alfanun gina madatusn ruwan ga al’uma ba, amma a cewar McCartney hakan ba dalili ba ne da zai sa mutane da ke zama a kusa da su su shiga halin kakanikayi, musamman idan aka yi la’akkari da cewa mutane miliyan 145 ne ke kamuwa da zazzabin cizon sauro a kasashen Afrika da ke Kudu da Hamada a duk shekara.

Saurari Karin Bayani.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG