Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyaye Akwai Bukatar Gyara Wajan Taya 'Ya'ya Zabar Abokan Aure -Inji Malama Lami Sumaiyya.


A cigaba da hirar mu da matasa akan irin rawar da iyaye ke takawa wajan sama masu abokan zama ko aure a takaice, mun sami zantawa da iyaye da dama harma muka taki sa'a malama Lami Sumayya Murtala, dattijiya kuma uwa ta bamu shawarwari harma ta yi kira ga iyaye akan lamarin.

Kamar yadda malamar ta fara bayani akan muhimmancin sanin tarihin juna, ta kara da cewa iyaye nada rawar da zasu taka mai matukar tasiri ga rayuwar 'ya'yan su musamman idan suka taimaka masu wajan samun aure nagari domin samun zuriya mai nagari.

Dattijiyar ta kuma yi kira ga iyaye da su tashi tsaye domin a cewar ta jama'a da dama sun manta da illar barin 'ya'ya kara nemarwa kansu matan aure. A cewar ta koda sun bar 'ya'yan su nemar wa kawunan su auren, to su tabbatar sun taya su bin diddigin gano asali da tarbiya domin samun zuriya mai nagari.

Daga karshe ta yi gargadi ga samari da 'yan mata da cewar lallai ya kamata idan zasu nemi aure to su tabbatar sun nemi izinin iyaye domin basu damar sa ido da kuma bincike domin taimaka masu.

Ga cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG