Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Dan Najeriya A Indiya Akan Zargin Damfara


Rundunar ‘yan Sandan kasar Indiya ta cafke wani dan Najeriya, da ake zargi da damfarar fiye da mutane tasa’in, a kasar ta Indiya.

Shi dai wannan dan Najeriya, mai suna Igwe Festus Abraham, dan shekaru arba’in da uku, da haihuwa maszaunin Malviya Nagar ne a Delhi babban birnin kasar ta Indiya.

Abraham dai ana zargin sa da damfarar mutane ne ta hanyar yaudararsu da chachar lottery, wanda hakan ya biyo bayan karar da wata mata ta kai wajen ‘yan Sanda.

Ita dai wanna mata Abraham ya nuna mata kudaden waje ne cewa ana bukatar sinadarin da za’a wanke su baya daya wanke mata biyu ya kuma bata kudi ta canja su zuwa kudin Indiya, daga nan ita kuwa sai ta amince dashi.

‘Yan Sanda sun gano cewa yana da ajiyar banki har guda goma sha hudu daban daban a mayan bankuna kasar indiya.

XS
SM
MD
LG