Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige ya bukaci matasan kasar da su kawar da idanun su daga neman aikin gwamnati, mai makon hakan su koyi sana’oi domin biyan bukatun rayuwa da na yau da kullum, wannan ya nuna matakin gwamnatin Buhari na cika alkawarin da tayi lokacin yakin neman zabe na samar da ayyukan yi lallai ya bullo ta wajan samar da ayyukan gwamnati ba, domin yanzu abin nema shine tabbatar da dukkan jahohi na iya biyan albashi akan lokaci ba tare da rage yawan ma’aikatan ba.
Ta dalilin haka ne gwamnatin ta fito da wani tsari na amfani da kudi rabin Naira Triliyon daya domin koyawa matasa maza da mata da masu fama da nakasa miliyan takwas sana’oi da kuma basu jari.
Ministan yada labarai na Najeriya Lai Muhammed da yake amsa tambaya kan wannan shiri da gwamnatin ta bullo da shi bayan tada farashin man fetur daga Naira Tamanin da Shidda zuwa dari da arba’in da biyar ya ce zasu shiga can kuryar yankunan karkarane, kuma zasu fara ne da kashi talatin cikin dari na kananan hukumomin Najeriya dari bakwai da saba’in da hudu.
Ko ta yaya gwamnati zata iya zabar mutanen da zasu amfana da wannan shirin? Ministan y ace zasu yi aiki tare da kungiyoyi masu zaman kansu da tun farko ke gudanar da ayyuka a yankunan, kuma dama suna da tarin bayanai daga hukumar zabe ta kasa, kuma zasu yi amfani dasu ta wajan isa ga wadannan mutane.
Ga cikakkiyar hirar.